A taƙaice: Prix Dan Gourmou, Gobara a Birnin ƙonni, ƙollo ƙafa…labaran wannan mako

 
Litinin 26 ga Oktoba, 2026


 

Yankin Agadez na shirin samar da tsarin tsara amfani da filaye

Yankin Agadez na shirye-shiryen samar da tsarin tsara amfani da filaye na farko.

A wannan ɓangare, tawagogi uku sun zagaya sassa daban-daban na yankin, tun daga ranar 12 ga watan Oktoba har zuwa ƙarshen makon da ya wuce.

Adamou Hamidou Garba, daraktan tsara yankuna da ci gaban ƙananan hukumomi na reshen Arlit, ya bada ƙarin bayani kan wannan shiri.

Muhimmancin kiyaye bayanai da kayayyakin sauti da fotuna

A daidai lokacin da ake shirin bikin ranar duniya ta kiyaye kayayyakin sauti da fotuna, a ranar 27 ga watan Oktoba, an mayar da hankali kan ƙalubalen adana irin waɗannan kayayyaki a tsarin zamanin dijital.

Bayanan sauti da fotuna da ake wallafawa a shafukan sada zumunta na haifar da tambayoyi dangane da yadda ake amfani da su da kuma hanyoyin adana su.

Ousmane Mamoudou, ɗan jarida ƙwararre a fannin aikin jaridancin intanet, ya bada ƙarin haske kan wannan batu.

 
Talata 27 ga Oktoba, 2026


 

Sharuɗɗan zaɓen wadanda zasu lashe kyautar gasar Prix Dan Gourmou

An fara gasannin kide kide da wake wake na Prix Dan Gourmou a ƙarshen makon da ya gabata, kuma za su ci gaba har zuwa ranar 29 ga watan Oktoba.

Taken gasar ta bana shi ne « L’artiste musicien au cœur de la Refondation du Niger », wato rawar da mawaƙi ke takawa a cikin aikin sake gina Nijar.

Daladi Adamou, daga ma’aikatar al’adu da fasaha, ya bayyana cewa ana amfani da sharuɗɗa da dama wajen zaɓen waɗanda za su lashe gasar.

Yayi ƙarin bayani kan waɗannan sharuɗɗa.

Baje kolin kayayyakin Albasa a Niamey

An gudanar da bikin ranar albasa ta kasa karo na shida daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Oktoba a birnin Niamey.

Bikin na bana ya mayar da hankali kan shigar matasa cikin ayyukan sarrafa kayayyakin noma zuwa abinci da kuma kasuwanci ta yanar gizo.

A wannan lokaci, an shirya baje kolin kayayyaki a zauren Stade du 29 Juillet, inda aka nuna kayayyaki daban-daban da aka sarrafa daga albasa. Wasu mata masu baje kolin kayayyakin sun yi ƙarin bayani.

 
Laraba 28 ga Oktoba, 2026


 

Gobara ta yi barna a kasuwar Birnin Konni

A daren Talata zuwa Laraba, wata gobara ta lalata wani ɓangare na kasuwar Birnin Konni, da ke cikin yankin Tahoua.

A cewar shugaban ‘yan kasuwa na birnin, duk da cewa ba a samu asarar rayukan mutane ba, amma an yi asarar dukiyoyi masu yawa.

Alhaji Ado Issa yayi ƙarin bayani kan wannan gobara da irin ɓarnar da ta yi.

 
Alhamis 29 ga Oktoba, 2026


 

Jami’ar Abdou Moumouni ta shirya ayyukan wayar da kai kan lafiyar Ƙwaƙwalwa

Jami’ar Abdou Moumouni ta Niamey ta shirya wasu ayyuka da safiyar Alhamis, a cikin tsarin bikin ranar duniya ta lafiyar Ƙwaƙwalwa, wadda ake gudanarwa a kowace ranar 10 ga watan Oktoba.

Manufar ayyukan ita ce wayar da kan al’umma  da kuma inganta hanyoyin kula da mutanen da ke fama da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa.

Dokta Jafar Hamadou, ƙwararre a fannin ilimin halayyar ɗan Adam kuma malami a jami’ar Abdou Moumouni, ya yi ƙarin bayani.

 
Juma’a 30 ga Oktoba, 2026


 

Nijar na halarta wasannin Olympics na Matasa a Dakar

Daga ranar 31 ga Oktoba zuwa 13 ga Nuwamba, birnin Dakar zai karɓi bakuncin Wasannin Olympics na Matasa. Wannan ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan taron Olympics a nahiyar Afirka.

Kimanin matasa ‘yan wasa 2,700 daga ƙasashe fiye da 200 za su halarci gasar. Nijar ma za ta samu wakilci, inda ‘yan wasa shida za su fafata a fannonin wasa biyar.

Salamatou Kadri ta kawo ƙarin bayani.

A gefe guda, Mena U15 ta kammala halartar gasar Coupe du Monde et Festival U15 a Azerbaïdjan da nasarar ci 3 da 2 a kan Afirka ta Kudu. Nijar ta kammala gasar a matsayi na 43 cikin ƙasashe 189 da suka halarta.

Nijar da Mali Baƙi na Musamman a SIAO 2026

An buɗe bikin baje kolin sana’o’in hannu na ƙasa da ƙasa na Ouagadougou, SIAO, karo na 18, a ranar 30 ga Oktoba. Za a ci gaba da gudanar da shi har zuwa ranar 8 ga Nuwamba 2026 a babban birnin Burkina Faso.

Taken bikin shi ne: « Artisanat africain et industrialisation : quelle synergie pour une meilleure organisation et valorisation des produits locaux et du patrimoine culturel ? wato aikin hannun Afrika da zamanintar kmafani : wane hada karfi domin wani kyautatuwar shiryawa da darajata kayayyakin gida da arzikin al’adu »

Nijar da Mali ne baƙi na musamman na wannan karo, yayin da Ghana ke matsayin ƙasar dake haskakawa. Ƙasashe 30 ne ke halarta, tare da rumfunan baje koli 700, kuma ana sa ran kimanin mutane dubu 500 za su ziyarci bikin cikin kwanaki goma.

An Kammala Prix Dan Gourmou Karo na 13 a Tahoua

Bayan kwanaki da dama na wasannin kiɗa da suka nuna bambancin al’adun kiɗan ƙasa, an kammala Prix Dan Gourmou karo na 13 a Tahoua da yammacin Alhamis, bayan sanar da sakamakon alƙalan gasar.

A rukunin mawaƙi ɗaya, yankin Tahoua ne ya lashe kyauta ta farko. Niamey kuma ta samu kyauta ta farko a rukunin ƙungiyar mawaƙa da kuma rukunin orchestra.

Masu shirya gasar da mahalarta sun bayyana ra’ayoyinsu game da sakamakon wannan karo. Za a ji bayanansu da Ibrahim Badagé ya tattara.