Litinin 2 ga Nuwamba, 2026
Direbobin Adaidaita Sun Shiga Yajin Aiki na Kwana Biyu a Tillabéri
A Tillabéri, direbobin baburan haya da aka fi sani da « Adaidaita » sun shiga yajin aiki na kwanaki biyu.
A cewar ƙungiyarsu, matakin na da nufin nuna rashin amincewa da wasu ƙa’idodin da hukumomi suka ɗauka, musamman waɗanda suka shafi hana babura wuce wasu shingayen ‘yan sanda da kuma shiga wasu unguwannin birnin.
Soumaila Morou, shugaban ƙungiyar direbobin baburan haya, ya bayyana damuwar direbobin.
Wasannin Olympics na Matasa: Nijar Ta Fara da Gasar Wushu
Nijar ta fara shiga gasa a Wasannin Olympics na Matasa na Dakar 2026 a ranar 1 ga Nowamba, a fannin wushu.
A karon farko da ya halarta, ɗan wasan Nijar Mahamadou Eggoh ya zo na 10 cikin mahalarta 12 a gwaje-gwaje biyu da aka haɗa, wato changquan da gunshu.
Mai horar da shi, Abdoulaye Eggoh, ya yi tsokaci kan wannan shiga ta farko.
Talata 3 ga Nuwamba, 2026
Hatsarin Hanya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 1,245 a Nijar a 2025
A Nijar, hatsarin hanya ya yi sanadin mutuwar mutane 1,245 a shekarar 2025, a cewar Hukumar ANISER. Kamfanin dillancin labaran Nijar, ANP, ne ya ruwaito wannan bayani a wallafarsa ta ranar 2 ga Nuwamba 2026.
A cewar wannan majiya, kashi 99.24 cikin ɗari na hatsarurrukan na da alaƙa da halayen mutane, ciki har da gudu fiye da kima, ƙin ba da fifikon hanya, rashin taka-tsantsan, rashin bin alamomin hanya, tuƙi cikin maye, ɗora kaya fiye da kima da kuma barci yayin tuƙi.
Farashin Wasu Nau’ikan Abincin Dabbobi Ya Ragu a Niamey
A Yamai, farashin wasu nau’ikan abincin dabbobi ya nuna alamar sauka zuwa ranar 31 ga Oktoba na 2026 idan aka kwatanta da watan Satumba, a cewar cibiyar kungiyoyin manoma.
Raguwar ta shafi musamman buhunan kilo 100 na ɓawon wake, ganyen gyada da na wake, da kuma buhunan kilo 25 na dusa da ake shigowa da ita daga Togo da Benin.
A cewar wannan majiya, hakan na da alaƙa da ingantuwar wadatar kasuwanni da kayayyakin noma na cikin gida. Sai dai wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga waje na ci gaba da fuskantar sauye-sauyen farashi da matsalar wadatuwa.
Laraba 4 ga Nuwamba, 2026
An Tsayar da 30 ga Nuwamba Don sakin Gonaki a Birnin Konni
Hukumomin gundumar Birnin Konni sun ayyana ranar 30 ga Nuwamba 2026 a matsayin ranar ‘sakin gonaki.
An bayyana hakan ne yayin wani ayarin wayar da kai kan zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.
Laftana Kanal Issa Yacouba, préfet na gundumar Konni, ya yi ƙarin bayani kan wannan mataki.
Yamai Ta Ƙayyade Amfani da Wuraren Jama’a Domin Kasuwanci
A cikin wata doka da aka fitar ranar 2 ga Nuwamba 2026, magajin gari na birnin Yamai, Kanal Boubacar Soumana Garanké, ya ƙayyade girka kayan kasuwanci a gefen manyan titunan babban birnin.
Daga yanzu, an hana yin kasuwanci a kan magudanan ruwa, titunan masu tafiya a ƙasa da wuraren da aka tanada domin zirga-zirga.
‘Yan kasuwar da suke kan waɗannan wurare tuni suna da wa’adin watanni biyu daga ranar 1 ga Nuwamba 2026 domin daidaita kansu da wannan mataki. Haka kuma, duk wani amfani da filin jama’a na ƙaramar hukuma zai buƙaci izini tun da farko.
Alhamis 5 ga Nuwamba, 2026
An Gudanar da Ranakun Manoman Shinkafa Karo na 16 a Yamai
An gudanar da Ranakun manoman shinkafa karo na 16 a Palais des congrès na birnin Yamai, bisa shirin kungiyar FUCOPRI.
Taken wannan karo shi ne: « L’implication des parties prenantes dans la gouvernance des sociétés coopératives selon l’Acte uniforme OHADA ».
Bachirou Issouffou, shugaban FUCOPRI, ya yi ƙarin bayani kan wannan taro.
Gobara Ta Shafi Mutane 981 a Gandun Dabino na Argui
A ƙaramar hukumar Dirkou, yankin Agadez, wata gobara da ta tashi ranar 24 ga Oktoba a gandun dabino na ƙauyen Argui ta shafi mutane 981 daga gidaje 173.
A cewar alkaluman babbar ma’aikatar kula da jariyar na ranar 28 ga Oktoba da kamapanin dillancin labaru ANP ya ruwaito, gobarar ta lalata itatuwan dabino 1,197 da lambunan kayan lambu 185.
Préfet na gundumar Bilma ya ziyarci wurin ranar 27 ga Oktoba domin duba ɓarnar da kuma ganawa da mutanen da abin ya shafa. A wannan ziyara, ya ba wa waɗanda suka yi asara taimakon kansa na CFA 200,000.
Juma’a 6 ga Nuwamba, 2026
Shugaban Mali Assimi Goïta Ya Kai Ziyarar Aiki Nijar
Shugaban riƙon ƙwarya na Mali, Janar Assimi Goïta, ya kai ziyarar aiki Yamai ranar Alhamis 5 ga Nuwamba 2026, bisa gayyatar takwaransa na Nijar, Janar Abdourahamane Tiani.
A cewar sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar bayan ziyarar, shugabannin biyu sun tattauna kan halin tsaro a cikin yankin kawancen kasashen Sahel, AES, da kuma yaƙi da ta’addanci. Sun kuma tattauna kan zirga-zirgar mutane da kayayyaki ba tare da cikas ba, bunƙasa ababen more rayuwa na sufuri, masana’antun noma da kuma amfani da albarkatun makamashi da ma’adinai.
Shugabannin biyu sun kuma bayyana aniyarsu ta ci gaba da ƙarfafa AES. A ƙarshen ganawar, shugaban Mali ya gayyaci takwaransa na Nijar zuwa ziyarar aiki a Mali, kuma an amince da gayyatar, inda za a tsayar da ranar ta hanyar diflomasiyya.
Taron Wayar da Kai Kan Shayar da Jarirai Nono a Tahoua
An gudanar da wani taron wayar da kai kan bunƙasa shayar da jarirai nono a wannan Juma’a a Tahoua.
Ma’aikatar Lafiyar Jama’a ce ta shirya taron, wanda ya haɗa hukumomi, ma’aikatan lafiya, ɗaliban makarantun lafiya da jama’a domin tattauna amfanin shayar da jarirai nono ga uwa da yaro.
Rayana Amadou, ƙwararriya kan abinci mai gina jiki a ma’aikatar lahiya ta jaha, ta bayyana abin da ake sa ran taron zai cimma.
Hoto – Fadar Shugaban Jamhuriyar Mali